Wednesday, 18 September 2019

Ruftowar Gini ya halaka Uwa da 'ya'yanta A jihar Yobe

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Jiya da misalin karfe 2:00 na dare ginin soro na kasa ya fadowa wani magidanci da iyalan sa a unguwar Tashar Machina dake hanyar asibitin FMC a Nguru dake jihar Yobe. Inda matar gidan ta rasa ranta tare da 'ya'yan ta guda biyu (mace da namiji). Shi kuma daya daga cikin 'ya'yan nata yana asibiti sakamakon jikatar da ya yi.Tuni dai aka yi jana'izar su yau Laraba.

Fatan mu Allah ya jikan su ya karbi shahadar su.
Rariya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment