Sunday, 15 September 2019

Sabon Salo: 'Yan Najeriya sun fara nada kansu mukaman masu baiwa masu rike da mukaman siyasa shawara


Wani sabon salo da ya fito a tsakanin 'yan Najeriya a dandalin Twitter shine na nada kansu mukaman masu bada shawara ga masu rike da mukaman siyasa. Sukan ce sun nada kansu mukamin masu bawa mutum shawara sannan kuma zasu yi aiki na tsawon wanni 3 kyauta sannan zasu aikawa mutum yanayin Albashin da zai rika biyansu, sukan karasa da cewa tuni har sun fara aiki.Daga cikin wanda aka wa wannan abu akwai gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da Bashir Ahmad, me baiwa shugaban kasa shawara kan sabbin kafafen sadarwa da Hadiza Bala Usman, Shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa na Najeria, NPA dadai sauransu.

Saidai daga cikin wadanda akawa wannan abu Bashir Ahmad ne kadai yayi magana zuwa lokacin wannan rubutu inda yawa wanda yace ya nada kanshi a matsayin me bashi shawara taya murna, alamar dake nuna kamar ya amince kenan.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment