Saturday, 7 September 2019

Samuel Eto'o Yayi Ritaya daga buga kwallo

Tauraron dan kwallon kasar Kamaru, Samuel Eto'o ya bayyana ritaya daga kwallo bayan da ya shafe shekaru 22 yana bugata. Dan shekaru 38 da ya lashe kyautar karramawa ta gwarzon dan kwallon Afrika sau 4 ya bayyana ritayar tashi ce ta shafinshi na Instagram.Ya saki wani hoto da yake cikin duhu inda ya rubuta an zo karshe, zamu durfafu wani kalubalen, Nagodemuku ku duka. Ina sonku.

Eto'o ya fara buga kwallo makarantar horas da 'yan kwallon ta Kadji Sport Academy dake Kamaru, daga nanne ya tafi Real Madrid. Ya kuma je kungiyoyi irin su, Leganes, Espanyol da Mallocar.

Eto'o ya kuma bugawa Barcelona da Inter Milan wasa, ya kuma bugawa Chelsea da Everton wasa, ya kuma yi wasa a kungiyoyin kasashen  Rasha,Italiya Turkiyya da Qatar.

A jimulla ya ci kwallaye 370 a wasanni 759 daya buga.

Ya dauku kofuna irin su, Champions League, Laliga, Copa del Rey Seria A dadai sauransu.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment