Tuesday, 17 September 2019

Sharhin wasannin Champions League: Liverpool ta sha kashi a hannun Napoli 2-0: Chelsea ta sha ci 1 a hannun Valencia

Tau yau an fara ta fa kuma wasanni sun dan yi ba zata, a wasannin farko da aka buga na gasar cin kofin Champions League a daren yau, Wasan da ya dauki hankula sosai shine na Chelsea da Valencia wanda sai da kawuna suka dauki zafi wayan minti 74 sannan Valencia ta saka kwallo daya bayan dawowa daga hutun Rabin Lokaci.
Chelsea ta samu damar rama kwallonta inda aka bata bugun daga kai sai gola ana mintuna 88, Willian yaso ya buga kwallon amma Ross Barkley ya nuna mai ya barshi ya buga saidai ya bugata ta yi sama bata shiga ragaba, a haka aka tashi wasan Valencia ta tafi da maki 3. Barkley ya buga bugun daga kai sai me tsaron gida sau 5 inda ya ci guda 3. Kuma wannan rashin nasara a wasan farko shine irinshi na farko a tarihin Chelsea, duk sauran masu horar da 'yan wasanta da suka gabata suna yin nasara a wasanninsu na farko banda Lampard.

Wasa na biyu daya dauki hankula shine tsakanin Liverpool da Napoli, shima wannan wasa an sha gumurzu inda har aka tafi hutun rabin lokaci babu wanda aka sakawa kwallo, bayan an dawone a minti 82,Valencia ta samu bugun daga kai sai gola ta ci, kuma ana minti 90 suka kara cin kwallo ta biyu, kuskuren tauraron dan kwallon baya na Duniya, Virgil Van Dijk ne ya jawo musu cin. Rabon da Liverpool ta yi rashin nasara a wasanta na farko tin kakar wasan 1994/95. Sannan kuma a karin farko cikin wasanni 74 daga buga a gasar Champions League, Liverpool bata kai hari ko daya me kyau ba a wasan na yau.

Wasa na gaba daya dauki hankula shine tsakanin Barcelona da Dortmund, an tashi wasan 0-0 kuma Messi ya buga wasan inda ya shigo ana kusan mintuna 30 a tashi, Matashin tauraron dan kwallon Barca, Ansu Fati ya buga wasan inda ya kafa tarihin kasancewa dan wasa mafi karancin shekaru daya buga gasar tun bayan Bojan. Dortmund ta samu bugun daga kai sai gola amma dan wansanta Marco Reus ya barar da bugun inda golan Barca, Ter Stegen ya tare kwallon.

Wasa na gaba shine wanda Salzburg ta ci Genk 6-2. Dan wasan Salzburg, Erling Haaland ya zama dan wasa mafi karancin shekaru na 3, bayan Raul da Rooney da ya ci kwallaye 3 a gasar Champions League, shekarar 19, su kuma shekarunsu 18 a sanda suka ci tasu.

Sai kuma wasan Inter Milan da Slavia Prague wanda aka tashi kunnen doki 1-1, dan Najeriya , Peter Olayinka dake bugawa Slavia wasa ne ya ci kwallon kuma shine dan wasan Najeriya na farko daya ci kwallo a wasanshi na farko a gasar Champions League tun bayan Yakubu da yaci kwallaye 3 a shekarar 2002.

Sauran wasannin da aka buga sune Ajax ta ci Lille 3-0

Sai Lyon da Petersburg 1-1


Sai Benfica data sha kashi a hannun  RasenBallsport Leipzig da ci 2-1
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment