Monday, 16 September 2019

Shin Abuja na fuskantar mamayar masu satar mutane?

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce babu barazanar tsaro a babban birnin kasar Abuja, sannan kuma masu garkuwa ba su mamaye birnin ba.


Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da rundunar ta fitar sakamakon wasu sakonni da ake yadawa a kafafen sadarwa musamman ma na sada zumunta, cewa ana samun karuwar aikata miyagun laifuka a ciki da wajen Abujar.

A 'yan kwanakin da suka gabata an yi ta yada sakonni a kafafen sadarwa da ke cewa an sace mutum shida a ranar 14 ga watan Satumba, da suka hada da wani malamin Jami'ar Baze da aka sace da tsakar rana, da wasu matasa biyu da aka sace da yamma a kan hanyarsu ta komawa gida daga Islamiyya a Wuse Zone 6.Sakon ya kara da cewa an kuma sace wata mata Mrs Hanna Azuibuike da misalin karfe 8.30 na dare a kusa da Habiba plaza a unguwar Maitama, sai kuma Ummi Umar Ardo wacce aka sace a wajen wani shago Blickers SuperMarket da ke Asokoro.

A cikin sakon an gargadi mutane tare da ja musu kunne cewa Abuja na fuskantar mamayar masu satar mutane don kudin fansa.

Amma rundunar ba ta bayar da bayanin satar dukkan wadancan mutane da sakon ya ambata ba, sai rundunar 'yan sandan birnin tarayyar a wata sanarwar daban ta tabo batun sace Ummi Umar Ardo, har ma kuma ta ce tuni ta kaddamar da bincike kan lamarin.


Sai dai a cikin sanarwar 'yan sandan shugaban rundunar M.A Adamu ya ce "birnin na cikin yanayi na tsaro ba kamar yadda mutane ke ta yadawa ba."

Ya kuma ce kamar a sauran kasashen duniya, Najeriya na da matsalolinta na tsaro.

Sai dai shugaban rundunar ya ce gudanar da bincike da yin kididdiga kan manyan laifuka da ake aikatawa a manyan biranen duniya zai bayyana cewa Abuja na daya daga cikin birane da ba a cika aikata laifuka ba.

M.A Adamu ya ce rundunar 'yan sandan birnin tarayya na da tsare-tsaren yaki da laifuka, wadanda kuma ake yawan ingantawa don tabbatar da tsaro.

Ya yi kira ga dukkan mazauna birnin da baki da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da fargaba ba.
BBChausa.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment