Tuesday, 17 September 2019

Shin Messi zai bugawa Barcelona wasan Champions League yau?

A yaune za'a fara buga gasar cin kofin Champions League tsakanin kungiyoyin turai, daya daga cikin wasannin da za'a buga a yau shine tsakanin Barcelona da Borussia Dortmund, saidai abinda ya fi daukar hankali a wasan shine ko Messi zai buga?Tun bayan da aka dawo kakar wasan bana Messi be bugawa Barca waa ba saboda raunin da yake jinya amma a Ranar Litinin shafin sada zumunta na Barcelona ya bayyana cewa Messi ya warki kuma an sakashi cikin wanda zasu buga wasan na yau.

Saidai da ake hira da me horas da 'yan wasan na Barcelona, Ernesto Valverde ya bayyana cewa basu yanke shawarar ko Messi zai buga wasan na yau ba ko kuwa a'a amma dai nan gaba zasu tsayar da shawara.

An dai saka matashin dan wasannan na Barca me shekaru 16, Ansu Fati cikin wanda zasu buga wasan na yau.

Zuwa an jima zamu ga idan Messi zai buga ko kuma a'a.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment