Monday, 16 September 2019

Shugaba Buhari ya aikewa da kasar Saudiyya jaje kan harin da aka kaiwa matatar man kasar

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya aike da sakon jaje ga kasar Saudiyya kan harin jirgi mara matuki da aka kaiwa matatar man kasar.A cikin wata sanarwa da me magana da yawun shugaban kasar,Malam Garba Shehu ya fitar shugaban ya bayyana cewa yana tare da sarkin Saudiyya a wannan yanayi da kasar ta samu kanta.

Yace Najeriya ta taba samun kanta a irin wannan yanayi inda aka kai mata hari kan kayan albarkatun manta, burin maharan shine durkusar da gwamnati amma burin su bai cika ba, kuma ba zasu taba cimma wannan burin nasu ba.

Ya kara da cewa, Duk da yake ba'a san ko waye ya kaiwa kasar ta Saudiyya hari ba amma wannan harine kan tattalin arziki wanda kuma zai shafi sauran al'umma.

Shugaban ya kara da cewa koma su waye maharan ba zasu samu magoya bayaba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment