Wednesday, 11 September 2019

Shugaba Buhari ya bayyana dalilin da yasa miliyoyin 'yan Najeriya ke fama da talauci

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana abinda ya jefa Miliyoyin 'yan Najeriya cikin talauci, tashin lafiya da hana wasu yara samun ilimi.
Shugaban yayi bayaninne ta bakin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustafa a wajan taron Akawu-Akawu na kasa karo na 49 da kungiyar kwararrun akawu ta Najeriya, ICAN ta shirya.

Ya bayyana cewa Cin hanci da rashawa ne ya jefa miliyoyin 'yan Najeriya cikin talauci da rashin lafiya da rashin isassun kayan aiki da likitoci a asibitocin mu sannan shine yayi sanadin rashin zuwan wasu yara makaranta.

Shugaban yace dan haka idan bamu yi maganin cin hanci ba yanda ya kamata ba zamu samu sakamakon da ake bukata ba.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment