Tuesday, 10 September 2019

Shugaba Buhari yayi rashin hadimin da ya mai hidima ta shekar 30


President Buhari loses domestic staff who served him for 30-years
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi rashin daya daga cikin masu mai hidima, Buhari Nalado Sandamu wanda yayiwa shugaban kasar da iyalanshi aiki na tsawon shekaru 30.

Da yake magana akan rasuwar hadimin nashi ta bakin me magana da yawunshi, malam Garba Shehu, shugaba Buhari ya bayyana cewa yayi rashin hadimi na kwarai me suna Kwamanda.

Shugaba yayi fatan Allah yawa marigayin hadimin nashi Rahama sannan ya baiwa iyalai da 'yan uwa Hakurin Rashi. Ya rasune a asibitin Aminu Kano.

Shugaban ya aikeda wakilai na musamman dan mika ta'aziyyarshi ga iyalab Kwamanda.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment