Friday, 13 September 2019

Shugaba Buhari zaikai ziyara kasar Burki Nafaso

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Burkinafaso inda zai halarci taron kungiyar habaka tattalin Arzikin yammacin Afrika ta ECOWAS a gobe Asabar.
Hakan na kunshe a sanarwar da me magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar a yau inda yace taron zai mayar da hankaline kan matsalar tsaron da yakin na na Afrika ta yamma ke fuskanta.

Shugaban zai samu rakiyar gwamna Abubakar Bello da Dapo Biodun da Okezie Ikpeazu na jihohin Naija, Ogun da Abia da sauran manyan jami'an gwamnati.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment