Wednesday, 18 September 2019

Shugaban Kasar Afganistan ya tsallake rijiya da baya batan da bam ya tashi a inda yake

Mutane 26 ne suka mutu sakamakon wani harin bam da aka kai a wajen taron gangamin siyasa da Shugaban Kasar Afganistan Ashraf Gani yake jagorantar gudanarwa.


Kakakin Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida Nasrat rahimi ya bayyana cewar an tayar da wnai bam da aka daura a jikin babur a tsakiyar jama'ar dake halartar gangamin a yankin jengel na jihar Parvan.

Ya bayyana mutuwar mutane 26 da suka hada da fararen hula 22, kuma wasu 42 sun jikkata sakamakon harin. 

Ana fargabar wasu za su kara mutuwa sakamakon yadda wasu mutanen 11 suka samu munanan raunuka.

Shaidun gani da ido sun ce Shugaban kasar Afganistan Ashraf Gani na wajen a lokacin da aka kai harin kuma ya kubuta da ransa da lafiyarsa.

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin.

A ranar 28 ga watan Satumban nan za a gudanar da zaben Shugaban Kasa a Afganistan.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment