Sunday, 15 September 2019

Sojin Najeriya 13 sun sake mutuwa a harin Boko Haram

Rahotanni daga Najeriya sun ce akalla sojojin kasar 13 ne suka mutu a cikin 'yan kwanakin nan, sakamakon karuwar hare-haren kungiyar Boko Haram wadda ta sauya sabon salo ta hanyar yiwa Sojin kwanton bauna a baya-bayan nan.
Majiyar Sojin Najeriyar ta sahaidawa jaridar Premium Times da ake wallafawa a kasar cewa, mayakan sun yi nasarar kwace tarin makamai daga hannun Sojin.

Bayanai sun ce mayakan sun fara kai hari kan sojin ne daga ranar Lahadin makon jiya yayinda rundunar sojin ta ki cewa komi game da batun, duk da tuntubar kakakinta Kanal Sagir Musa.

Majiyar ta ce daga cikin wuraren da aka kai harin har da Gajigana da Kukawa.

Rahotanni sun ce Babban hafson sojin kasar Janar Yusuf Tukur Burutai ya ziyarci Maiduguri inda ya gana da shugabannin Sojin.
RFIhausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment