Tuesday, 17 September 2019

Sojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Jami'ar Maiduguri

Rahotanni daga Najeriya sun ce rundunar sojin kasar ta yi nasarar dakile wani harin ta'addanci da kungiyar Boko Haram ta shirya kai wa Jami'ar Maiduguri cikin daren jiya Lahadi, inda aka rika jin karar harbe-harbe a makarantar.
Majiyoyi daga makarantar sun ce an kusan sa'a guda da rabi ana jiyo karar harbin indiga da ke nuna musayar wuta tsakanin Sojin da mayakan na Boko Haram, kafin daga bisani al'amura su daidaita.

Rahotanni sun ce wasu daliban makarantar da ke jarabawa sun yi kokarin barin makarantar cikin dare domin tsira da rayukansu.

Ko a jiya akwai wasu labarai da jaridun Najeriyar suka wallafa wanda ke nuna yadda harin na Boko Haram ya hallaka Sojin kasar 13.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment