Sunday, 15 September 2019

Sowar kin jini ya katse jawabin shugaban Afrika ta kudu a Zimbabwe

Shugaban kasar Afrika ta kudu, Cyril Ramaphosa ya nemi afuwar al’ummar Afrika yayin jawabin da ya gabatar a wajen makokin tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe a yau Asabar, bayan da taron jama’a suka rika yi masa kuwwa da kalaman nuna kyama.

Yayin jawabin nuna alhini da Ramaphosa ya fara gabatarwa ihu da sowar nuna kin jininsa ya cika wajen taron makokin yayinda yayi saurin juya jawabin nasa zuwa na neman yafiya da kuma nuna bacin ransa game da hare-haren nuna kin jinin baki da ke faruwa a kasarsa.

Akalla mutane 12 aka kashe cikin watan nan sanadiyyar hare-haren da al’ummar kasar Afrika ta kudu ke kaiwa kan baki ‘yan kasuwa da ma’aikata a birnin Johannesburg da sauran sassan kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa ihu da kalaman nuna kin jinin kan shugaban Ramaphosa sun hana shi kammala jawabansa na makokin Robert Mugabe da ya mutu a cikin makon jiya yana da shekaru 95 a duniya bayan fama da jinya tsawon lokaci.
RFIhausa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment