Tuesday, 10 September 2019

Ta bankawa kanta wuta ta mutu saboda an hanata kallon kwallo

Wata mata 'yar kasar Iran ta bankawa kanta wuta bayan da aka hanata shiga kallon wasan kwallon kafa.Matar me suna, Sahar Khodayari 'yar shekaru 29 taje shiga kallon wasan inda jami'an tsaro suka zargeta da yin shigar maza kuma aka kamata.

An kaita kotu dan yanke mata hukunci, saidai kotun ta daga sauraren karar, bayan daga kararne, Sahar ta zubawa kanta fetur ta kuma cinnawa kanta ashana ta kone ta mutu a ranar Litinin din data gabata.

Tun bayan juyin juya hali na shekarar 1979 kasar Iran ta haramtawa mata shiga filin wasa dan kallon kwallo.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta HRW ta yi Allah wadai da wannan lamari inda ta yi kira ga hukumar kwallon kafa ta Duniya data dauki matakai masu tsauri da zasu kawo karshen hana mata zuwa kallon kwallo a kasar IRAN.

Wata 'yar uwar Sahar ta bayyana cewa tana fama da nau'in tabin hankali ba me tsanani be, dake zuwa yana tafiya kuma kamata da aka yi ya taso mata da wannan ciwo.

Itama dai hukumar FIFA ta aika da sakon ta'aziyyarta ga iyalan Sahar inda tace tana kira ga kasar Iran da ta janyewa mata wannan haramcin.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment