Sunday, 8 September 2019

Tammy Abraham be isa ya sani zama a Benci ba>>Olivier Giroud

Dan wasan gaba na kungiyar Chelsea, Olivier Giroud ya bayyana cewa sabon matashin dan wasan kungiyar da aka dauko daga makarantar horas da 'yan wasan kungiyar,Tammy Abraham be isa ya mayar dashi zama a benci ba.
Tun bayan zuwanshi Chelsea, Giroud dan shekaru 32 yana ta kokarin ganin ana fara wasa dashi a wasannin kungiyar saidai ya kara gamuwa da cikas saboda zuwan Tammy Abraham dan shekaru 22 wanda kuma zuwa yanzu ya ciwa Chelsea kwallye 4 a gasar Premier League shi kuwa Giroud be ci ko daya ba.

Hakan yasa aka mai tambayar shin yana ganin cewa Abraham zai iya sa a mayar dashi zama a benci.

Yace wannan sam ba zai taba yiyuwa ba duk dai cewa yazone ya zama abin koyi da kuma baiwa matasan 'yan wasa karfin gwiwa amma be yi ritaya ba kuma har yanzu yana da yunwar cin kwallo, kamar yanda ya gayawa Le Figaro.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment