Sunday, 8 September 2019

Tauraron dan kwallon Chelsea ya sha dukan kawo wuka bayan da yayi yunkurin yiwa budurwar wani dan wasa magana

Tauraron dan kwallon kafar kungiyar Chelsea, Danny DrinkWater da a yanzu yaje kungiyar Burnley Aro ya sha dukan kawo wuka bayan da yayi yunkurin yiwa budurwar wani dan kwallo magana a wani gidan rawa.Danny ya je gidan rawar ne inda yake taya wani abokinshi murnar zagayowar ranar haihuwarshi, sai yayi abinda ya saba, watau yayi tatul da giya, yana cikin maye sai ya nufi budurwar dan kwallon kungiyar, Scunthorpe United, Kgosi Ntlhe yana mata magana.

Yayi ta binta duk inda ta yi har saida ya kureta ta mai tsawa inda tace ya mata shiru, saboda tare take da saurayinta. Nan ne sai ga saurayin nata suka fara cacar baki da Danny har ta kai ga naushe-naushe.

Jami'an tsaron gidan rawar sun fitar da su duka biyun daga gidan rawar inda a wajenne abu ya kazance. Wasu matasa da ake tunanin suna bayan Kgosi ne suka taru sukawa Danny dukan kawo wuta inda suka tattaka mai kafa, kamar yanda wata majiya ta gayawa Mail.

Majiyar tace Danny be san yanda abin ya kasance ba dan baya cikin hayyacinshi a lokacin, saida abokanshi suka bashi labari da safe sannan ma yasan ainahin abinda ya faru.

Danny na cikin mawuyacin hali kamar yanda majiyar ta kara da cewa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment