Monday, 9 September 2019

Tsananin zafi ya kashe mutane kusan 1500 a Faransa

Zafin da aka samu wanda ya fi na kowanbe lokaci tsanani cikin watan Yuni da Yuli a Faransa ya kashe mmutum 1,435 a wannan shekara.


Faransa ta fuskanci zafin da ya kai 46c a ma'aunin zafi, abinda ba ta taba fuskantar irin haka ba a tarihi.

Ministar lafiya ta kasar Agnes Buzyn, a lokacin da ta tattauna da wata kafar yada labaru ta ce akasarin wadanda suka mutu sanadiyyar zafin suna da kimanin shekara 75 ne.
Sai dai Ms Buzyn ta ce matakan kariya da mutane suka dauka sun taimaka wajen rage mace-macen, wanda ta ce ya yi kasa idan aka kwatanta da na shekarar 2003.

Ma'aikatar lafiya ta kasar Faransa ta ce mutum 567 suka mutu a sanadiyyar tsananin zafi da aka fuskanta na farko a kasar tsakanin 24 ga watan Yuni, zuwa 7 ga watan Yuli.

Sai kuma wasu mutanen 868 suka mutu lokacin da tsananin zafin ya sake dawowa tsakanin ranakun 21 zuwa 27 ga watan Yuli.

A watan Yulin wannan shekara babban birnin kasar Paris, ya fuskanci zafin da ya kai 42.6c.

A lokacin zafin dai gwamnati ta shawarci jama'a da su dauki matakan kariya.

An kuma rufe makarantu da wuraren taruwar al'umma.

An samu zafi mai tsanani da ya zarce na kowane lokaci a baya a kasashen Turai, irin su Birtaniya, da Belgium, da Jamus, Luxembourg da kuma Netherlands.
BBChausa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment