Wednesday, 18 September 2019

Tun kamin a Hadu Kocin Atletico Madrid ya tsorata da Ronaldo, ji abinda yace

Me horas da 'yan wasan kungiyar Atletico Madrid, Diego Simeone ya bayyana tauraron dan kwallon Juventus wanda dadadden abokin hamayyar kungiyarshine, Cristiano Ronaldo a matsayin dan wasa me matsala.



A hirar da yayi ta kamin fara wasa ya bayyana cewa Duk Sanda Ronaldo ya rike kwallo yakan zama matsala kuma abune mu wuya a iya tareshi, yana da tarihin bajinta ta ban mamaki,injishi.

Ya kara da cewa musamman ifan Ronaldo ya matsa kusa da raga, matsalarshi na karuwa sosai, saidai yace abu mafi dacewa shine mutum ya shiga filun da tunanin cewa zai yi nasara.

Ya kara da cewa kuma kwallo bata da tabbas kowa zai iya baka matsala. Juventus dai yau zata je gidan Atletico Madrid inda zasu buga wasan farko a kakar wasan bana ta Championa League.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment