Sunday, 8 September 2019

Wani malamin Addinin kirista dan kasar Afrika ta kudu ya fasa kwai kan harin kyamar baki na kasar

Wani fasto a kasar Afrika ta kudu ya bayyana cewa hare-haren da ake kaiwa mutane a kasar Afrika ta kudu tabbas na kyamar bakine ba kamar yanda gwamnatin kasar ke kokarin kawar da hankalin mutane ba cewa wai harin na wasu tsageru ne.Malamin addinin me suna, Buti Tigagale ya bayyana cewa a garuruwa irinsu Pretoria da sauransu an samu rahotannin mutanen gari sun rika kaiwa mazaunan kasar 'yan kasashen waje hari da kwasar kayan ganima a shagunansu a gaban jami'an tsaro ba tare da an dauki wani mataki ba hakanan a ranar da abin ya faru gwamnati bata dauki wani tsatstsauran mataki ba akan lamarin.

Yace idan ana maganar cewa wai masu sayar da kwayane ai akwai masu sayar da kwaya 'yan asalin kasar me yasa su ba'a kai musu hari ba?

Ya kara da cewa maganar gaskiya 'yan kasar Afrika ta kudu suna da kyamar baki irin ta 'Yan Nazi na kasar Jamus saidai yace kashi 80 na mutane  'yan kasar kiritocine kuma abinda bibul ya koya musu shine babu banbanci tsakanin mutum da mutum kowa na Yesu Almasihune.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment