Tuesday, 10 September 2019

Watanni 8 kenan tun kamin zabe da bude tashar jirgin ruwa ta Baro amma har yanzu bata fara aiki ba

Watanni 8 kenan tun bayan da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da bude tashar jirgin ruwa ta Baro dake karamar hukumar Agaie Jihar Naija dan ta fara aiki amma har yanzu shiru.A watan janairun da ya gabatane, kamin a gudanar da babban zaben shugaban kasa, Buhari ya je ya bude tashar amma watanni 8 bayannan har yanzu bata fara aiki ba.

Daily Trust ta kai ziyara wannan tasha inda ta zanta da wasu mazauna gurin da suka bayyana maya cewa sun yi tsammanin harkar kasuwanci da aka saba gani tun lokacin turawan mulkon mallaka zai dawo amma har yanzu shiru.

A shekarar 2011/12 ne gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar gyara tashar ruwan akan Naira Biliyan 5.8 amma saboda rashin sakin kudin aikin, sai aiki ya tsaya, amma bayan zuwan shugaba Buhari mulki an saki kudin aka kammala aikin.

Wani Captin Hassan Muhammad me ritaya dake dan garinne ya bayyana cewa watanni 8 kenan har yanzu ko jirgi daya be zo tashar ba, yace ta yaya jirgi sai zo tashar yayin da babu manyan jami'an gwamnati ko daya kamata su yi aiki a tasha?

Akwai dai bukatar ma'aikata irunsu jami'an kwastam dana shige da fice da sauransu da ya kamata ace suna tashar amma babu kowa.

Akwai kuma sauran matsaloli da suka hana tashar ruwan fara aiki irin su rashin kyakkyawan titi da kuma tashar bata da wutar lantarki wani janareta ne da bazai iya daukar ayyukan tashar ba aka jiye a gurin.

Kwarru masu sharhi akan al'amuran yau da kullun sun bayyana cewa suna tsoron tashar kawai an yi amfani da itane wajan cimma burikan lashe zabe an kuma yi watsi da ita.

Hukumar kula da tashoshin ruwa ta NIWA ta bayyanawa Daily Trust cewa rashin kyawun hanyane ya hana fara aiki a tashar ta Baro kuma sun aikewa da ma'aikatar ayyuka da korafi sunce suna kan duba lamarin.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment