Saturday, 14 September 2019

Yadda aka sace mazaunin makewayin gwal a fadar Blenheim

An sace wata mazaunin makewayi da aka kera da zinare mai nauyin ma'aunin karat 18 a fadar Blenheim.


Wasu gungun 'yan fashi ne suka yi awon gaba da mazaunin na gwal bayan sun kutsa cikin gidan da ke Woodstock a Birtaniya.

Mazaunin na daga cikin kayan da aka bude bajekolinsu a ranar Alhamis, wanda masanin kere-keren kayan alfarma dan kasar Italiya, Maurizio Cattelan ya shirya.

Ya zuwa yanzu ba a san inda mazaunin yake ba amma 'yan sanda na tsare da wani mutum dan shekara 66 bisa zarginsa da hannu a fashin mazaunin na gwal.Satar ta haifar da ''gagarumar barna da ambaliya'' saboda an riga an hada shi da layin ruwan ginin, a cewar 'yan sanda.

Fadar Blenheim wacce aka gina tun a karni na 18 na daga cikin wuraren tarihi na duniya, kuma ita ce mahaifar Sir Winston Churchill. Yanzu haka an rufe fadar domin gudanar da bincike.


Wata jami'ar 'yan sanda a kasar, Jess Milne ta ce "abin da aka sace a wurin baje-kolin wani mazaunin makewayin gwal ne da aka kera da zinare kuma yana da matukar tsada."

"Muna kyautata zaton cewa bata garin sun yi amfani da akalla mota biyu a lokacin da suka aikata wannan ta'asar."

"Zuwa yanzu ba a riga an gano inda mazaunin yake ba, amma muna gudanar da cikakken bincike domin mu gano shi kuma a gurfanar da masu hannu a ciki a gaban kuliya."

A cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, Fadar Blenheim ta ce za ta dakatar da aiki har zuwa karfe biyu na rana sakamakon abin da ya faru "ba zato, ba tsammani".

An yi wa Shugaba Donald Trump na Amurka tayin shahararren mazaunin makewayin a 2017.

Babu wanda ya samu rauni sakamakon fashin, kuma mutumin da aka kama na tsare a hannun 'yan sanda.
BBChausa.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment