Wednesday, 11 September 2019

'Yan Boko Haram basu da matsuguni a Najeriya>>Buratai

Shugaban sojin Najeriya,Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa Rundunar sojin Najeriyar ta hana kungiyar Boko Haram samun matsuguni a Najeriya saboda jajircewarta.Buratai yayi magana a gurin wani taro a babban birnin tarayya Abuja inda da aka yi kan gudummuwar jami'an tsaro ga ci gaban kasa.

Yace 'Yan Boko Haram basu da matsuguni a Najeriya yanzu saboda matsin da sojoji suka musu, yace sojoji da yawa manya da kanana sun rasa rayukansu wajan tsare Najeriya kuma zasu ci gaba da yin hakan dan ganin ana ci gaba da samun tsaro.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment