Sunday, 15 September 2019

'Yan kasar Afrika ta kudu sun fara zanga-zangar lumana dan baiwa 'yan Najeriya hakuri kan harin kyanar Baki

Bayan da akawa shugaban kasarsu ihu a kasar Zimbabwe wajan jana'izar Robert Mugabe, 'yan kasar Afrika ta kudu sun fito kan tituna suna zanga-zangar lumana ta baiwa 'yan Najeriya da sauran kasashen Afrika hakuri kan hare-haren kyamar bakin da aka kai musu.A wani bidiyo daya watsu sosai a shafukan sada zumunta anga 'yan kasar ta Afrika ta kudu a kan titi suna wakokin hadin kan Afrika da kuma rike da rubuce-rubuce na nuna adawa da hare-haren kyamar baki.

Hakanan bayan da aka mai ihu a Zimbabwe shima shugaban kasar ta Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya shirya wasu wakilai na musamman su 3 da ya tura kasashen Najeriya, Nijar, Ghana, Senegal, Tanzania, Congo da Zambia dan su aike da sakonshi na cewa yana tare da wadannan kasashe kuma su bayyana musu irin shirin da gwamnatinshi take na ganin ta shawo kan wannan matsala.

Kalli bidiyon zanga-zangar anan:


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment