Sunday, 8 September 2019

'Yan kasar Afrika ta kudu sun sake fitowa da makamai suna zanga-zangar 'yan kasar waje su bar musu kasa

'Yan kasar Afrika ta kudu a birnin Johannesburg sun sake fitowa a yau Lahadi dauke da makamai suna zanga-zangar neman 'yan kasar waje da su bar musu karsu.

Sowetanlive ne suka ruwaito labarin inda sukace mutanen da farko zasu hadune inda wani tsohon jagoran jam'iyyar neman 'yanci zai musu jawabi, yayin da suke kan hanyar tafiya zuwa wajan da zai musu jawabinne sai suka fara wake-wake suna kiran 'yan kasar waje su fice su basu guri.

Wannan yayi sanadiyyar aka samu sabon rikici wanda ya watsu zuwa wasu sassa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment