Thursday, 12 September 2019

'Yan Najeriya 187 sun dawo daga kasar Afrika ta kudu:Gwamnati ta musu shiri na musamman[Kalli Hotuna]

Jirgin daya kwaso 'yan Najeriya 187 daga kasar Afrika ta kudu saboda gudun harin kyamar baki da ake kai musu ya sauka a filin jirgin jihar Legas a daren jiya, Laraba.Da farko dai an samu tsaikon zuwan jirgin na awanni 7 wanda hakan yasaka mutane cikin damuwa inda daga baya aka samu labarin cewa mahukuntan kasar ta Afrika ta kudune suka so su bada matsala.

Kamfanin jirgin Airpeace ne ya bayar da jirgi kyauta dan yin jigilar 'yan Najeriyar dake son dawowa gida daga kasar Afrika ta kudun saboda harin kyamar baki da ake kai musu acan.

Bayan dawowarsu an kai 'yan Najeriyar wani masauki na musamman da aka tanadar musu sannan kuma me kula da 'yan Najeriya dake kasashen waje, Abike Dabiri Erewa ta bayyana musu cewar akwai 'yan kudin da za'a baiwa kowannensu Naira dubu 40 sannan kuma da katin waya dan su kira 'yan uwansu.

Sannan ta kara da cewa akwai shiri na bankin masana'antu na BOI da zai zo ya koyar da wadanda ke son koyon kananan sana'o'i dan su dogara da kansu sannan za'a basu jarin da zasu fara dashi.

Wasu daga cikinsu sun bayyana irin mawuyacin halin da suka tsinci kansu a kasar ta Afrika ta kudu.

Wani dan jihar Osun, Saheed ya bayyanawa The Nation cewa, kawai dan yana dan Najeriya aka koreshi daga kamfanin da ya shafe shekaru 5 yana aiki.

Shima wani dan jihar Edo, Anthony Joshua ya bayyana cewa 'yan kasar Afrika ta kudun basu da mutunci ya kamata Najeriya ta yanke huldar jakadanci da su.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment