Monday, 16 September 2019

'Yan Najeriya 2 sun mutu a cikin jirgin sama bayan da kwayar da suka sha ta fashe musu a ciki

Wasu Inyamurai 'yan Najeriya su 2 da suka hadiyi kwaya sun mutu bayan da kwayar da suka hadiya ta fashe a cikin cikinsu yayin da suke cikin jirgin sama.Mutanen biyu wanda aka bayyana da sunayen Chigozie Pascal Aniagbado da kuma Chijioke Chidioka Obuefi suna cikin jirgine daga kasar Brazil zuwa Kasar Ethiopia tafiyar awanni 12.

Wanda ya bayar da labarin yanda lamarin ya faru yace yana zaune tsakiyar mutane 2 sai dayan ya tambayeshi dan Allah ya duba mai taswirar jirgin yaya tagiyarsu? Ya duba ya gayamai cewa sun yi rabin tafiyar.

Ya kara tambayarshi ko yana jin Inyamuranci? Sai suka ci gaba da magana inda yace mai baya tunanin za'a sauka dashi a jirginnan saboda kwayar dake cikinshi ta lallace zata iya mai illa. Nan yace sai ya fara kyarma, mutumin ya gayamai cewa kada ya tada hankalinshi kwayar a cikinshi take, nan ya bukaci ya mikomai ruwa.

Amma sai yaki tashi saboda gudun kada ya tashi ya sakamai kwaya a jaka. Saidai ya daga hannu ya kira ma'aikatan jirgin suka kawo mai ruwa, ya bukaci abinci aka bashi, sai kuma ya fara kyarma y fadi kasa, yace nan likitoci suka taru a kanshi ana tambayar kasar da ya fito da kuma yarenshi, ana cikin hakane sai shoma wani can ya fara irin wannan yanayi.

Me bada labarin yace jirgin yayi kokarin saukar gaggawa amma saboda kasar da suke akwai Ibola sai suka ki sauka, jimawa kadan sai duk mutane biyun suka mutu.

Kalli bidiyon lamarin a kasa:Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment