Friday, 13 September 2019

'Yan Najeriya 22,000 sun yi batan dabo>>ICRC

Hukumar bayar da agaji ta Red Cross ta ce akwai kusan 'yan Najeriya 22,000 da har yanzu ba a gano inda suke ba, a yayin da aka yi fiye da shekara 10 ana fama da rikice-rikicen Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.


ICRC ta kiyasta cewa kusan kashi 60 cikin 100 na mutanen dai yara ne lokacin da suka bace.Wasu kuwa sun rasa 'yan uwansu ne sakamakon guduwa da mutane suka dinga yi daga yankin, yayin da wasu kuma suke tsare har yanzu.


Shugaban hukumar ta ICRC Peter Maurer, wanda ya kammala wata ziyara a kasar a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, ya ce ya kamata a kara kokari wajen gano inda suke, domin a bai wa sauran mutane da ke neman 'yan uwansu damar sanin makomarsu.

Mista Maurer ya ce "Suna kananan yara a lokacin da suka bata, hakan na nufin dubban iyaye ba su san inda yaransu suke ba, ko suna raye ko a mace," kamar yadda ya fada ranar Alhamis a lokacin da ayke jawabin ban kwana bayan shafe kwana biyar a Najeriya.

"Babu babban tashin hankali ga iyaye irin batan 'ya'yansu. Wannan shi ne halin tashin hankalin da dubban iyaye ke ciki a Najeriya," in ji shi.

Najeriya dai na fama da rikice-rikice daban-daban da suka hada da hare-haren kungiyar Boko Haram da kuma rikici tsakanin manoma da makiyaya.

Rikicin Boko Haram ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasata cewa fiye da mutum 27,000 ne suka mutu yayin da mutum miliyan biyu kuma suka rasa muhallansu a arewa maso gabashin Najeriyar sakamakon rikicin na Boko Haram.
BBChausa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment