Wednesday, 11 September 2019

'Yan Shi'a 31 sun mutu a turmutsutsun Ashura

Akalla mutum 31 ne suka mutu a wani turmutsutsu a lokacin tunawa da ranar Ashura da mabiya Shi'a ke yi a birnin Karbala na Iraqi, kamar yadda jami'ai suka bayyana.


Wani mai magana da yawun ma'aikatar lafiya ta kasar ya ce akwai wasu mutanen 100 da suka samu raunuka, amma kuma ya ce akwai yuwuwar yawan wadanda suka rasun ya karu.

Rahotanni sun ce an samu turmutsutsun ne lokacin da wani daga cikin dubban mutanen da ke ibada ya fadi, sai aka yi ta fadawa kan juna.Ranar Ashura wato goma ga watan daya na shekarar Musulunci, rana ce ta tuna shahadar da jikan Manzon Allah (SAW), Imam Hussein ya yi a yakin Karbala, a shekara ta 680 ta miladiyyar annabi Isa (AS).

Kowace shekara miliyoyin Musulmi mabiya Shi'a ke zuwa birnin Karbala domin tuna ranar ta Ashura, inda suke ayyuka na ibada da kuma kwaikwayon shahadar da Imam Husseinin ya yi.


Wani kakakin ofishin watsa labarai na lardin Karbala ya gaya wa BBC cewa a lokacin da dubban mabiyan ke wani gudu na ibada, wanda ake kira Gudun Tuwairij, sai wani mutum ya yi tuntube ya fadi, wanda hakan ya sa sauran jama'a suka yi ta faduwa.

Sai dai kuma wani jami'in tsaro ya sheda wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press, cewa turmutsutsun ya auku ne bayan da wata hanya ta rufta.


A shekara ta 2004 sama da mutane 140 ne suka mutu a wasu jerin hare-haren bam da aka kai kusan lokaci daya a wurin ibadar a Karbala da kuma Bagadaza a lokacin gangamin na Ashura.

Shekara daya bayan wannan kuma, akalla masu ibada 965 ne suka rasa rayukansu a lokacin wani turmutsutsu a kan wata gada ta kogin Tigris a Bagadaza, a lokacin bikin wata ranar ta daban ta mabiya Shi'ar.

Mutane sun tsorata da dimaucewa saboda rade-radin da aka yada a lokacin cewa 'yan kunar-bakin wake ne suka shiga taron.
BBChausa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment