Sunday, 8 September 2019

'Yan Shi'a sun sha alwashin fitowa Tattakin Ashura: 'Yansandan sunce su fito su gani

Duk da haramta ayyukan kungiyar da kotu ta yi, kungiyar shi'a ta IMN ta bayyana cewa zata fio ranar Talata dan yin bakin cikin kashe jikan manzon Allah(S.A.W) Hussain Ibn Abi Talib.
'Yan Shi'a kanyi tattaki a fadin Duniya duk 10 ga watan Muharram saboda wannan rana kuma na Najeriya ma sun bayyana cewa zasu fito su yi duk da haramta ayyukansu da kotu ta yi da kuma umarnin da shugaban 'yansanda na kasa ya bayar na kamasu da ruguza gine-ginensu.

Me magana da yawun kungiyar, Ibrahim Musa ya bayyanawa Punch cewa, tuni ma 'yan shi'a da yawa a wasu jihohin Najeriya suka fara bikin Ashura amma har yanzu babu rahoton cewa an kama ko guda daya kuma ranar talata zasu fito a Abuja da sauran jihohin Najeriya dan wannan tattaki.

Yace a shirye suke su sdaukar da rayuwarsu duk da ceea su ba fada suka fito yi ba shiyasa suke fitowa da 'ya'ya da matayensu, idan ma an samu wani abu to jami'an tsarone zasu kawoshi, yace kuma suna nan Najeriya babu inda zasu.

Saidai hukumar 'yansanda ta hannun me magana da yawunta, Frank Mba yace 'yan shi'qr su fito suga abinda zai faru.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment