Tuesday, 17 September 2019

'Yan ta'addar Boko Haram sun kashe sojoji 5 a Kamaru

Sojoji 5 sun rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai kan sansanin dakarun kasa da kasa na hadin gwiwa a yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru.


Labaran da jaridun kasar suka fitar sun rawaito Janaral Bouba Dobekreo na rundunar hadin gwiwar ta kasa da kasa na cewa 'yan ta'addar sun kai wa wata cibiyar sojoji hari dake tsibirin Soureran na tafkin Chadi.

Dobekreo ya ce bayan kai harin ne arangama ta barke inda aka kashe sojoji 5 tare da jikkata wasu 8.
TRThausa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment