Sunday, 8 September 2019

'Yan wasan Barca za su hada kudi domin ceto Neymar daga PSGNeymar
Wasu daga cikin 'yan wasan Barcelona sun yi tayin yin amfani da kudadensu wajen sayen tsohon abokin taka ledarsu dan kasar Brazil mai shekara 27, Neymar daga PSG a lokacin bazara bisa yakinin da suke da shi cewa idan ba Neymar to zai yi wa kulob din ya samu nasara a gasar Champions League. (Marca).


Juventus zai fara tattaunawa da mai tsaron ragar Manchester UnitedDavid de Gea a watan Janairu, lokacin da kwantaraginsa da kulob din zai kare, in ji jaridar (Sunday Express).
Man United din dai na gab da kammala duk mai yiwuwa wajen nada tsohon mai tsaron ragarta dan asalin kasar Netherlands, Edwin van der Sar a matsayin darektan kwallo na kulob din, kamar yadda (Sunday Mirror) ta rawaito.
Real Madrid za ta yi kokarin sayen dan wasan gaba dan faransa, Kylian Mbappe mai shekara 20 dagaParis St-Germain a bazara mai kamawa. (Sport - in Spanish)
Manchester City za ta taya dan wasan Inter mIlan mai shekara 24, Milan Skriniar a watan Janairu, a kokarin Pep Guardiola na magance matsalar da suke da ita a bayansu. (Sunday Express)
Virgil van Dijk, mai shekara 28, ya amince da sabuwar kwantaragin shekara shida da Liverpool.(Sunday Mirror)
Dan wasanJuventusna gaba, Juan Cuadrado, mai shekara 31 zai fara tattaunawa da kulob din domin sanin makomarsa bayan da kwantaraginsa za ta kare. (Goal)
Dan wasan gaba dan asalin kasar Ingila mai shekara 20, Eddie Nketiah, na gab da koma wa Leeds United daga Arsenal domin sama wa kansa kujera a kulob nan gaba, (Mail on Sunday)
ManajanSevillaJulen Lopetegui na son sayen dan Nacho Fernandez, dan kasar Spaniya mai shekara 29 daga Real Madrid a lokacin bazara. (Marca)
Napoli na shirin tsawaita kwantaragin dan wasan kasar Spaniya na baya, Fabian Ruiz a kulob din. Idon kulob din Real Madrid dai na kan dan wasan mai shekara 23. (Football Italia)
BBChausa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment