Sunday, 8 September 2019

Yanda zaka sace zuciyar budurwarka ta ji kai kadai take so

A kwai mutumin da kawai kana ganinshi zaka ji ya maka kana sonshi akwai wanda shima daga ganinshi watakila zaka yi tunanin taku ba zata taba zuwa daya ba, watau soyayya ta tsakani da Allah da bata da wani gauraye wadda turawa ke cewa unconditional Love, saidai duk da haka a zahiri yake cewai akwai abubuwan da ke sa a so mutum.

Na farko dai idan an fito karara ance ba'a sonka to gaskiya inaga ka hakura yafi.

Amma idan dai zata saurare ka inaga ta baka damar ka tallata kanka ko ciniki zai kaya.

Na daya dai shine kalamai wanda suna da matukar muhimmanci a soyayya, ka rika gayawa masoyiyarka cewa kana sonta sosai, a farkon soyayyarku kada ka damu da saita rika mayar maka da kalaman soyayyar da kake mata, idan soyayyar ta fara nisa itama ta fara sonka, zaka ga ta fara murmushi idan ka mata kalaman sannan daga baya har ta rika mayar maka.

Akwai kuma 'yan matanda (duk da basu da yawa saboda kunya) suma kai tsaye sukan fara gaya maka kalaman soyayya, AKwai budurwata da, bayan dana dauki lokaci ina mata kalaman soyayya, a haduwarmu ta biyu, kamin in ce mata ina sonta ita ta fara cewa tana sona, wanan misaline dake nuna cewa kalamai nada tasiri sosai a soyayya, musamman kalamin cewa ina sonki, ka yawaita maimaitashi akai-akai, guraren da ya kamata ka yawaita faden wadannan kalamai sune a lokacin da masoyiyarka ta faranta maka, da kuma lokacin da zaku rabu da kuma haka kawai koda kuna zaune kuna hira zaka iya cikin bazata ka kutso da kalmar.

Yabo, duk mutum yana son yabo, musamman mata, na daya dai ka lura da wani abu data keyi dake burgeka, iya maganane, tafiya, kyau, kunya, girmamawa, hakuri, dadai sauransu ka rika yaba mata akai-akai akan wannan abu, idan ta yi kwalliya ka yaba, idan kaji kanshin turarenta ka yaba, ka rika gaya mata irin muhimmancin da take dashi a zuciyarka, da dalilan da suka sa kake sonta, misali saboda gidansu gidan mutuncine, suna da tarbiyya dadai sauransu. Kada ka boye irin son da kake ji a zuciyarka, wannan motsin da kake ji a zuciyarka idan ka tunata ko kuma idan kuna magana, bazai misaltuba, ka gaya mata hakan, ka kuma gaya mata cewa kana sonta, idan kaji irin wannan motsi a zuciyarka kuma bakwa tare, ka dauki waya ka aika mata da gajeren sako me cewa kana tunaninta yanzu haka. Karka yawaita kiranta ko zuwa tadi da yamma lokacin girki ko kuma tsakar rana, saboda da tsakar rana idan aikine yayi zafi, idan kuma ba aiki, lokacin hutune, da yamma kuma akwai girki. Mafi dacewar lokacin kiran soyayya, musamman lokacin da ake renonta shine da sassafe kamin a fara aikin aikin gida, da kuma da yamma can kusa da magariba, sai kuma da dare kamin lokacin bacci. Kada ka yawaita korafi akan duk kuskuren da ta yi, ka rika kauda ido. Ka rika kurantata sosai.

Kwalliya: Mata na son namiji me tsafta, ka rika kokari kana tsaftace abin hawanka in kuma baka dashi ka rika yin shigar zamani, shigar zamani bawai tana nufin kananan kaya ba kawai, koda shadda ko yadi zaka saka ya zamana an maka dinkin zamani ka sha turare.

Kyauta: Kyauta tana daya daga cikin abubuwan dake jawo da kuma karfafa dankon soyayya, ka rika wa budurwarka kyautar kudi, musamman in da hali sabbi, ka kula da abinda take so na amfani ko na ci ka rika siyo mata, lokaci-zuwa lokaci, ka rika sai mata Cakulan, biskit na zamani me daukar hankali, Ice Cream, Cake, Burger, Pizza, kai koda babu irin wadannan abubuwa na zamani a garinku ko a unguwarku,ba za'a rasa cakula ko alewa ba, ko tsire ko balangu wanda kowa ke maganarshi saboda dadinshi, ka rika siya mata shi, lokaci zuwa lokaci. Ka rika mata kyautar ba zata a lokacin da bata tsammani.

Duk da wannan na san wasu zasu kalubalanceshi, dan haka ka tambayeta idan za'a barta a gida, idan kana da abin hawa, lokaci zuwa lokaci zaka iya daukarta zuwa guraren shakatawa na garinku, amma ta kasance tare da kanwa ko kaninta. Idan baku da gurin shakatawa kuna iya rika zuwa wajan cin abinci na zamani me kayatarwa, idan duk baku da wannan a garinku, kana iya daukarta zuwa bakin rafi haka Da yamma.

Ka rika nuna mata kulawa, kana damuwa da damuwarta. Misali, ka rika tambayarta maganar makaranta da kuma abinda take so ta zama nan gaba, ka rika kokarin ganin kana bata gudummuwa wajan cimma wannan buri nata, hakanan kaima ka rika gaya mata burin da kake son cimma nan gaba da kuma irin abinda kake son mata nan gaba. Ka rika cika mata alkawari idan ka dauka. Kada ka yawaita karya ko kuma ka yi karyar da zata tashi ka ji kunya, misali ka rika karyar abinda ba ka dashi ko kuma kana kai kanka inda baka kaiba, amma dai wajan kurantata da dan abinda ba'a rasa ba wannan zaka iyayi dan jan hankalinta. Ka rika kokarin yin barkwanci dan bata dariya.

Ribar soyayya itace aure, muddin kana sonta da gaske zaka so ta zama matarka, dan haka ka yi kokarin a sanka a gidansu dan kada wani ya maka shigar sauri. Sannan shi aure nufin Allah ne tana iya yiwuwa ku gama soyayyar amma ba itace matarka ba, saboda wasu dalilai dan haka sai ka barwa Allah zabi.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

1 comment: