Tuesday, 17 September 2019

'Yansandan Jihar Kano sun kama matashin daya kashe mahaifinshi me shekaru 80

'Yansanda a jihar Kano sun kama wani matashi dan shekaru 35 me suna Habibu Ibrahim daya kashe mahaifinshi, malam Ibrahim Salihu me shekaru 80 har lahira ta hanyar caka mai wuka.
Me magana da yawun 'yansandan na jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da manema labarai lamarin inda yace Habibu ya cakawa mahaifin nashi wukane da dare kuma an garzaya dashi Asibiti amma da misalin karfe 6:30 na safe sai ya rasu.

Lamarin ya faru a karamar hukumar Doguwa dake jihar.

Me magana da ywun 'yansansan Yace Habibu ya tsere bayan da lamarin ya faru, dan uwanshi, Yahaya ne ya kaiwa jami'an tsaro Rahoto inda aka kamoshi daga baya.

An Bayyana Habibu da cewa yana shaye-shayen miyagun kwayoyi wanda sanadiyyar hakane ma bayan yasha kwayar ya kashe mahaifin nashi.

Kwamishinan 'yansandan jihar Kano, Ahmad Iliyasu ya bayar da umarnin kai Habibu bangaren bincike na hukumar.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment