Friday, 13 September 2019

Yanzu Zan Iya Yi Wa Shekarau Wakar Yabo Tunda Ya Dawo APC>>Mawaki Rarara

Fitaccen mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara wanda a baya ya rika ragargazar tsohon Gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau saboda sauya jam'iyyar siyasa, a yanzu ya shaida cewa zai iya yi masa wakar yabo tunda ya dawo APC. 


A yayin zantawa da kafar sadarwa da yada labarai ta Sirrinsu Media, Rarara ya bayyana cewa sun zauna da Sanata Shekarau tare da tattaunawa wasu muhimman bayanai.

Ya ce "mun tattauna da shi kuma ya tabbatar min za mu hada hannu da shi. Ya ce ko yanzu wani abu ya taso Sardauna ya ce zai yi mana a zaman Da muka yi da shi".

Rarara ya kara da cewa "ni fa dama ina gaba da Shekarau ne saboda ba ya jam'iyyar da nake kuma ba ya tare da shugaba na. Amma yanzu mun hada hannu ko yanzu zan iya yi masa waka".

Kalli bidiyon hirar a kasa:
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment