Monday, 9 September 2019

Zakzaky da matarshi zasu sake fita kasar waje neman magani

Ana sa ran kwanannan shugaban kungiyar Shi'a ta IMN, Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarshi zasu sake fita kasar waje neman magani.

Kasashen da ake maganar zasu je sune Indonesia ko Malaysia kamar yanda me magana da yawun kingiyar ta IMN, Ibrahim Musa ya shaidawa The Nation.

Yace be da tabbacin kasar da suka yanke shawarar zasu je amma yasan tsakanin Malaysia ne ko Indonesia.

Ya kuma tabbatar da cewa, Gobe talata kungiyar zata fito dan yin tattakin ranar Ashura dukda hanin 'yansanda.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment