Monday, 9 September 2019

ZALUNCI DA RASHIN IMANIN SHUGABANNIN KASATA NIJERIYA

1. Lokacin da mutane sama da milyan hamsin (50,000,000) ke gaza cin abinci sau biyu a wuni.

2. Lokacin da yara sama da milyan uku (3,000,000) ba sa iya zuwa makaranta saboda talauci.


3. Lokacin da ma'aikata ke neman a rika biyan su N30,000 mafi karancin albashi a wata.

4. Lokacin da talakawa marasa lafiya sama da mutum dubu ashirin da biyar (25,000), ke mutuwa saboda rashin kudin sayen magani.

5. Lokacin da wutar lantarki ta gagari unguwannin Malam Talaka.

6. Lokacin da ruwan sha mai tsafta ya fi karfin Talakawa.

7. Lokacin da ake yawan samun haduran da ke lankwame rayukan daruruwan mutane saboda mutuwar tituna.

8. Lokacin da Talakawa sama da milyan dari (100,000,000) ke gararanba da kamfar rashin tartibin muhalli.

9. Lokacin da ayyukan yi suka gagari dan Talaka a muhimman wuraren gwamnati.

10. Lokacin da Malam Talaka ke mantawa da dinka sutura shi da ahalinsa.

Lokacin ne 'yan majalisun kasarmu su dari hudu da sittin da tara (469) kacal! Suka bukaci a saya musu motocin hawa na kimanin naira bilyan biyar da milyan hamsin (N5.05b) don kawai su rika hawa.

Hakika! Wannan babban abin bakin ciki ne da takaici da kuma nuna rashin kulawa daga jagororinmu.

A matsayina na dan kasa, mai kishinta da son cigabanta, ba na goyon bayan wannan yunkuri na 'Yan majalisa, kuma ina kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Ahmed Ibrahim Lawan, da na Majalisar Dokoki Femi Gbajabiamila, da kar su kuskura su amince da wannan yunkuri. 

Allah Ta'ala Ya taimaki Talakan Nijeriya!
Allah Ta'ala Ya taimaki Nijeriya!

Daga Muhammad Lawal Barista
8 Muharram, 1441 A. H.
8th September, 2019 C. E.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment