Monday, 7 October 2019

A rika daukar masu Addu'a na gida bana kasar Saudiyya ba>>Shehu Sani


A jiyane dai labarai suka watsu cewa gwamnan Borno,Babagana Zulum yayi hayar malam kasar Saudiyya su yiwa jihar tashi addu'a kan hare-haren Boko Haram, kamin nan shugaban soji, janar Tukur Tusuf Buratai ma yayi kira da'a yi amfani da addu'a wajan kawar da Boko Haram din.Wannanne dalilin da yasa tsohon sanatan Kaduna ta tsakinya,Shehu Sani ya bayyana cewa tunda an koma yin addu'a wajan magance matsalar tsaro ya kamata a rika daukar masu yin addu'a na gida Najeriya ba na kasar Saudiyya ba, ba wai shinkafa ce kawai za'ace dole a ci 'yar gida ba.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment