Saturday, 12 October 2019

Aikin Samar da wutar Lantarki na Kano ya kusa kammaluwa[Kalli Hotuna]

Aikin samar da wutar Lantarki na Jihar Kano dake Tiga ya kusa kammaluwa inda aka ce yanzu ya kai mataki na kaso 90 cikin 100 na kammaluwa.
Aikin samar da wutar zai samar da Megawat 10 na wuta kuma tsohuwar gwamnatin jihar ce ta fara shi inda a yanzu gwambatin Gwamna Ganduje ta ci gaba dashi. Gwamnan ya tabbatar da cewa kwanannan, nan da watanni 2 zuwa 3 za'a kammala aikin.

Aikin zai samar da wutar lantarki ga masana'antun jihar da da kuma wutacen kan tituna dake jihar. Kwai kuma irin wannan aikin da gwamnatin ke yi a Dam din Challawa.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment