Thursday, 17 October 2019

An bayyana Macen data fi kowace mace kyau a Duniya, Kalli hotunanta

Tauraruwar tallar kaya, Musulma, 'yar kasar Amurka, Bella Hadid ce aka bayyana a matsayin macen da ta fi kowace mace kyau a Duniya.
An yi amfani da wani lissafin kimiyyane na mutanen kasar Girka dake bayyana kyawun fuska me suna " Golden Ratio of Beauty Phi" wanda kuma Isabella ta samu maki 94.35.

Saidai an bayyana cewa matsalar Bella guda daya tal itace goshinta.

Me biyewa Bella wajan kyau itace shahararriyar mawakiyar kasar Amurkarnan watau Beyonce wadda ita kuma ta samu makin kyan fuska a lisaafin kimiyyar da ya kai 92.44.

Ta uku itace 'yar Fim kuma me tallar kayan sawa, Amber Heard wadda ta samu maki 91.85.

Sai ta 4 wadda itama mawakiyace watau Ariane Grande wadda ta samu maki 91.81.

Mawakiya Taylor Swift ce ta zo ta 5 inda ta samu maki 91.64

Likitan gyaran fuska na kasar Ingila, Dr Julian De Silva ne ya fitar da wannan kiyasi kamar yanda The Mail ta ruwaito.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment