Tuesday, 8 October 2019

An kashe mutane 4 ta hanyar bude a wata mashaya dake Amurka

Mutane 4 sun rasa rayukansu yayinda wasu 5 suka jikkata sakamakon bude wuta kan wata mashaya dake jihar Kansas din Amurka.


Tashar talabijin ta KSHB-TV ta bayar da labarin cewar da daddare ne a garin Kansas City wani ya bude wuta kan mutane a wata mashaya.

'Yan sanda sun ce mutane 4 sun mutu yayinda 5 suka jikkata sakamakon bude wutar da ba a san waye ko su waye suka yi ba.

'Yan sanda sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike kuma za a sanar da jama'a sakamakon da aka samu.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment