Tuesday, 29 October 2019

An yi barazanar tayar da bam a wurare 5 dake New York

A birnin New York na Amurka an yi barazanar tayar da bam a cibiyoyin 'yan kwana kwana da raba magungunan gaggawa guda 5.


A labaran da aka fitar an rawaito Rundunar 'Yan sandan New York na cewar a cibiyoyin kwana-kwana 5 dake yankin Manhattan na New York ne aka yi barazanar tayar da bam da misalin karfe 15.30.

An bayyana cewar bayan samun labarin barazanar ne jami'an 'yan sandan suka kwashe dukkan jama'ar dake gine-ginen.

Sanarwar da ofishin yada labarai na 'yan sandan New York ta fitar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike da nazari kan lamarin.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment