Tuesday, 8 October 2019

Barcelona ta kori koci kuma tsohon dan wasanta

Barcelona ta sallami kocin tawagar matasan ta ta ‘yan kasa da shekaru 19 Victor Valdes ba tare da bata lokaci ba, bayan rade – radin sa – in – sa tsakaninsa da daraktan matasa na kungiyar Patrick Kluivert.
A watan Yulin wannan shekarar Valdes ya koma Barcelona don jan ragamar karamar tawagar, shekaru biyar bayan ya bar kungiyar a matsayinsa na mai tsaron raga.

Dan shekara 37 ya kasance cikin jiga –jigan tsaffin ‘yan wasan kungiyar bayan shekaru 12 masu cike da nasara da ya yi a kungiyar, in da ya ci kofunan La Liga 6 da na zakarun Turai 3.

Rahotanni na cewa ba Kluivert ne kawai mutumin da ke gutsiri – tsoma da Valdes ba a kwanaki 80 da ya yi yana jan ragamar tawagar, sauran jami’ai ma ba sa jin dadin yadda yake tafiyar da harkokin atisaye.

An kara tada jijiyoyin wuya lokacin da tsohon mai tsaron ragar Spain din ya zake cewa za ayi salon wasan wasa na 4-4-2 maimakon 4-3-3 da take amfani da shi a matakin matasa.

Patrick Kluivert da Victor dukkanninsu tsaffin ‘yan wasan Barcelona ne.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment