Friday, 11 October 2019

Bindiddigi: Shin da gaske Buhari zai kara 'aure'?

A 'yan kwanakin nan, ma'abota shafukan sada zumunta na zamani a Najeriya sun ta yada labarin cewa shugaban kasar, Muhammadu Buhari zai kara 'aure' kuma ministarsa ta ma'aikatar ayyukan agaji da kula da bala'i, Sadiya Umar farouk zai 'aura'.


Wannan labarai dai ba a san daga inda ya fito ba amma zancen da ake ta yi kenan a ko'ina a fadin kasar inda har a shafukan sada zumunta an kirkiri wani maudu'i mai taken #BUSA2019, wato auren Buhari da Sadiya a shekarar 2019.

Ta kai har an saki wani katin gayyatar daurin auren shugaban da ministarsa inda aka nuna cewa ranar Juma'a 11 ga watan Oktoba ne za a 'daura auren' a babban masallacin da ke cikin fadar shugaban kasa.

Sai dai BBC ta samu bayanai daga wani makusancin fadar shugaban kasar wanda ba ya so a bayyana sunansa kuma ya musanta wannan labarin a kan cewa Shugaba Buhari ba zai kara aure ba.An kuma ta yada hotunan Muhammadu Buhari da Sadiya Umar Farouk wadanda suka dauke a can baya a lokacin ayyuka daban-daban. Kuma wadannan hotunan ne ake amfani da su don nuna sahihancin labarin.

Har ta kai an shirya wani bidiyo da hoton ministar da shugaban kasar kuma an dora wakar soyayya a kan bidiyon.


Wani mai amfani da shafin twita, mai suna Hamdollars ya sa hoton Sadiya Umar Farouk da babbar jami'a a Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed a wajen wani taro a birnin Geneva suna tsaye.

Amma sai ya bi hoton da wani sako mai ce "Ki bi shi sau da Kafa Sadiya, in yace yi, kiyi in yace bari ki bari, Ki zauna da yar uwar ki lafiya, kar kuyi tashin hankali, ko da an tsokane ki ki danne zuciyar ki, zaman aure seda hakuri''.

Haka kuma, an ta yada hotuna da bidiyon Sadiya Umar Farouk a wurin wani biki inda take rawa kuma ana yi mata liki da kudi. Masu amfani da shafukan zumunta sun yayata cewa taron 'bikinta' da shugaba Buhari ne.


Wani bidiyo ya bayyana, inda wata da ake zargin cewa Aisha Buhari matar Shugaba Buhari ce ta ke ta bambamin fada a harshen turanci.

Hoton bidiyon da ya nuna matar a tsaye sanye da doguwar riga, kuma ba a nuna fuskarta ba sai da jikinta.

A bidiyon an jiyo matar tana cewa wata mata "Me yasa za ku rufe kofar nan, me na yi maku ne? Fadar shugaban kasa ce nan, muna da sama da sojoji 200 da 'yan sanda 200 da ke tsare da mu. Hakan ya isa. Zan so in san lokacin da za ki bar wajen nan. Hakan ya isa."

Ita kuma matar da ake wa fadan tana ta fadin "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, ba wanda ya ce mana za ki zo gwoggo."


Mutane da dama dai na ganin cewa an dauki wannan bidiyon ne a daren Alhamis bayan da matar shugaban kasar ta iso fadar gwamnatin kasar watau Aso Rock ta tarar da kofofin dakinta a rufe.

Ire-iren wadannan sakonni dai sune suka mamaye shafukan sada zumunta a wannan makon a Najeriya.

Shin mene ne gaskiyar lamarin?
BBC ta samu bayanai daga wani makusancin fadar shugaban kasar wanda ba ya so a bayyana sunansa kuma ya musanta wannan labari.

"Zancen kara auren Shugaba Buhari ba gaskiya ba ne. Ba haka zancen yake ba," a cewarsa.

Sai dai ya ce matar shugaban kasar Aisha Buhari ta dade ba ta kasar. Asali ma, cewa ya yi ta shafe wata hudu a birnin Landan.

Majiyar ta ce an dade ana 'takun saka' tsakanin shugaban da matarsa, kuma watakila abin da yasa taki dawowa gida kenan .

Dangane da bidiyon da ya nuna wata mata tana fada a cikin wani gida kamar Aso Rock, majiyar ta tabbatar da cewa Aisha Buhari ce.

Sai dai majiyar ta ce tsohon bidiyo ne kuma an fi shekara biyu da daukarsa.

Kawo yanzu dai, fadar Shugaban Kasar bata ce komai ba kan wanna batun , haka ita ministar bata fitar da wata sanarwa don musantawa ko tabbatar da lamarin ba.

Sai dai Minista Sadiya Umar Farouk ta wallafa wasu hotuna da sakonni a shafinta na tuwita a ranar Alhamis da ke nuna cewa tana birnin Geneva don halartar wani taro.


Abin da kuma ke kara nuna cewa zancen auren ba gaskiya ba ne - tunda zai yi wuya a daura aurenta ba ta kasar, sannan kuma bidiyon da ake cewa na bikinta ne sun tabbata ba gaskiya ba.

Wasu daga cikin bidiyon ma an dauke su ne, lokacin da take murnar rantsar da ita a matsayin minista.

Hukunci

Daga bayanan da BBC ta tattaro daga majiyoyi da dama a fadar shugaban kasa, sam babu kanshin gaskiya game da batun cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai kara aure a ranar Juma'a 11 ga watan Oktobar 2019.

Sai dai kuma majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa akwai 'rashin jituwa' tsakanin matar shugaban, watau Aisha Buhari da wasu daga cikin dagin shugaban a waje daya - da kuma wasu makarrabansa a fadar gwamnatin kasar ta Aso Rock.

Hakan kuma na da nasa ba da shawarar da Aisha Buharin ta yanke na shafe watanni da dama a kasar waje a maimakon kasancewa tare da maigidanta a fadar Aso Rock da ke Abuja.
BBChausa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment