Monday, 7 October 2019

Boko Haram: An rufe makarantar Dapchi saboda tsoron hari

Fargabar hare-haren kungiyar Boko Haram ta sa an rufe makarantar sakandaren 'yan mata da ke garin Dapchi a jihar Yobe da ke Arewa maso-gabashin Najeriya.


Hukumar makarantar da kungiyar iyayen daliba makarntar ne suka ba da sanarwar rufe makarantar na wani lokaci.

Bayanai daga Dapchi na cewa iyayen yara sun samu rahoton harin da ake zargin kungiyar Boko Haram ta kai garin Babban Gida na karamar hukumar Tarmuwa a jihar a karshen makon da ya gabata.

Sai dai Babban sakatare na ma'aikatar ilimi ta jihar Yobe, Modu Aji ya shaida wa BBC cewa a hukumance ba a rufe makarantar ba, amma sun yi magana da shugabar makarantar, wadda ta tabbatar da wannan mataki da suka dauka.

A karshen makon da ya gabata ne wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram, suka kai hari a garin Babban Gida da ke makwabtaka da Dapchin.

Maharan sun kona gidan mai garin, sannan suka tafi da motarsa.Harin ya sanya fargaba da tsoro a zukatansu, wanda ya sa daga bisani hukumar makarantar da iyayen yara cimma shawarar rufe makarantar na wani lokaci.

"Muna nan a firgice domin sojojin sun tafi sun bar 'yan sanda. Sai dab da magariba da suka ji yaran sun fita sun bar Babban Gida tukuna suka dawo cikin gari.

"Amma 'yan sandan muna tare da su a cikin gari, da ikon Allah kuma babu abin da ya faru. Haka muke cikin garin Dapchi muna tsorace Allah Ya kare na gaba.

"Yaranmu dai sun tafi gida gaba daya," inji wani daga cikin iyayen yaran.

Sai dai Modu Aji ya ce ma'aikatar ilmi na jira shugabar makarantar ta kai musu batun rufe makarantar a rubuce.

"Yanzu a hukumance makarantar a bude take. Iyayen sun ce sun rubuta wasika za su kawo. Idan muka duba wasikar za mu nemi mu zauna da su sai mu samar da hanyar da hankalin kowa zai kwanta.

"In ma ta kama sai a inganta matakan tsaro idan suka ga akwai alamar barazanar tsaro. Amma yanzu akwai sojoji da 'yan sa kai a wurin," inji shi.

Ya kuma ce za a kara zama a tattauna da iyayen tun da ga dalilin da su iyayen ke bayarwa na dauke daliban daga makarantar.

Wani shaida ya fada wa BBC cewa a watannin baya ma an rufe makarantar sakamakon fargabar kai wa garuruwan da ke makwabtaka da makarantar hari.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin rundunar tsaron hadin gwiwa mai yaki da Boko Haram amma abin ya ci tura.

A watan Fabrairun 2018 ne dai wasu 'yan kungiyar Boko Haram suka sace dalibai mata sama da 100 daga makarantar.

Daga baya kungiyar ta sako 'yan matan 106 da kuma namiji daya, amma ta ki sakin Leah Sharibu.

Kungiyar ta sha yin barazanar kashe dalibar wadda ta ki sauya addininta.

Hukumomi da kungiyoyi na ta kira da a yi dukkan mai yiwuwa wurin karbo Leah Sharibu daga hannun kungiyar.

Gwamnatin Najeriya ta ce tana iya bakin kokarinta na ganin an sako dalibar cikin koshin lafiya.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment