Saturday, 12 October 2019

Fassarar Mafarke-mafarken Da Nake Yi Kan Gwamna Elrufai

Har yanzun ban samu nayi ido biyu da Malam Nasiru Elrufai ba, amma saboda mutane daga garuruwa da dama masoya Elrufai sun damu suna so na fassara musu mafarkin da na yi akan Malam shine na yanke shawara zan fassara wannan mafarkin, amma da na yi ido biyu da shi na tabbata saboda murnar wannan mafarkin da na yi a kan shi da ya yi min babbar kyauta.


Mafarkin da na yi na farko shine, ranar 08\9\2014 lokacin gwamna Ramalan Yero a Kaduna kafin a yi zaben 2015 ina cikin bacci kawai na yi mafarki Ramalan Yero ya zo wajen taro, yana zuwa sai El-rufai shi ma ya zo wajen, amma kawai na ga mutane suna ta ihu suna cewa Kaduna sai Malam. Kawai na farka a lokacin amma ban kawo abun a raina ba. Kawai bayan zabe na ga El-rufai ya zama gwamnan Kaduna. 

Wannan mafarkin duk bai bani mamaki ba. Sai ranar 10\6\2018, ina cikin bacci kawai na yi mafarki wata mata ta je gidan Malam Nasiru El-rufai tana zuwa ta fashe da kuka ta ce masa dan Allah ya taimake ta tana so ta zama tana da alfarma, sannan tana so ta dinga aiki da shi saboda ta yi tunani idan ta zama wani abu nan gaba za ta taimakawa mata yan'uwanta. Saboda ta lura yanzu siyasar ba a yi da mata.

Kawai sai na farka amma ban dauki wannan mafarkin wani abu ba. Saida na ga an yi zabe 2019 na ga El-rufai ya dauko wannan matar da na yi mafarki a kanta ya ba ta mataimakiyarsa. Kuma a tarihin siyasar Kaduna ba a taba baiwa mace mataimakiyar gwamna ba.

Mafarki na uku, na yi mafarki Malam Nasiru ya je wata makarantar firamare ya zauna a bakin aji yana ta kuka jama'a suka taru a kan shi ana tambayar shi me ya faru amma bai gayawa kowa ba. Ina farkawa daga bacci abun yana ta ba ni mamaki. Ashe wannan mafarkin da na yi alamar Malam Nasiru zai maida yaron shi makarantar gwamnati ne. Kuma hakan ya faru.

Mafarkin da na yi na karshe shine, na yi mafarki Malam Nasiru ya je Abuja Baba Buhari ya rike hannun shi yana ta sa masa albarka yana cewa kasata kasata kasata kasata

Wannan mafarkin shine yake ta ba ni mamaki har yanzu.

Ga lambar matashi Nazifi (Zuri)
08069413640Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment