Tuesday, 8 October 2019

Gwamna Masari Ya Nada Mataimakinsa Na Musamman Kan Mawakan Zamani

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya nada Ukashatu Suleman, wanda aka fi sani da Ajuba a matsayin mataimaki na musamman kan mawakan zamani.
Jawabin nadin na kunshe ne a wata takarda da Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa ya sanyawa hannu. Wanda nadin ya fara aiki tun daga 3 ga Oktoba. 

Wannan dai shi ne karo na biyu da ba shi wannan mukamin.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment