Saturday, 12 October 2019

Hazikin Soja, Rayyanu Muhammad, Mai Biyayya Ga Mahafiyarsa Ya Rasu A Fagen Daga

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Muncyi rashin dan uwa a fagen Daga Rayyanu Muhammad bawan Allah salihi mutumin kirki. Mahaifiyarsa tana matukar alfahari da shi, domin babu wata kyautatawa da yake tsallakewa face sai ya yi mata, a yanzu haka yana ginawa mahaifiyarsa katafaren gida.


Rayyanu wanda dan asalin jihar Bauchi ne, ya rasa rayuwansa a garin Warri dake jihar Delta, bayan wani kwantan bauna (Ambush) da wasu da ake zargi barayin man fetur ne, an ce su 16 ne suka rasa rayuwarsu a yayin farmakin.

An samu nasarar ceto gawarsa a cikin jigin ruwan dake dauke da shi da sauran jami'ansu wadanda suka suka rasu. An yi masa jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a garin Warri.

Allah ya jikansa da rahama. Amin.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment