Friday, 11 October 2019

Hukumar kwallon Spain ta haramtawa Dambele buga wasanni 2

Dan wasan gaba na Barcelona, Ousmane Dambele ba zai buga wasan El Clasico na farko tsakaninsu da Real Madrid ba, biyo bayan hukuncin haramta masa wasanni da kwamitin da’ar hukumar kwallon kafar Spain ya yanke masa.
A ranar lahadin da ta gabata, alkalin wasa ya baiwa Dambele jan kati, yayin wasan da Barcelona ta soke Sevilla da kwallaye 4-0, saboda kalaman rashin da’ar da ya furtawa mai alakalncin wasan Mateu Lahoz, bisa wani hukunci da ya yanke yayin wasan.

Wannan ce tasa a jiya laraba, kwamitin da’ar hukumar kwallon kafar Spain haramtawa Dembele buga wasanni 2.

Hukuncin na nufin Dambele ba zai buga wasan da Barcelona za ta yi tattaki zuwa Eibar ba a ranar 19 ga wannan wata na Oktoba, sai kuma fafatwar El Clasico da Real Madrid a gida, ranar 26 ga watan na Oktoba.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment