Sunday, 13 October 2019

Ji Martanin A'isha Buhari da aka tambayeta kan mutuwar aurenta da kuma yi mata kishiya

A’isha Buhari, uwargidar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ta dawo gida Najeriya da asubahin yau dinnan Lahadi, bayan an daina jin duriyarta na wani lokaci mai tsawo.


Ta gaya ma wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina a filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Ezikiwe da ke Birnin Tarayyar Najeriya Abuja, da sauran ‘yan jarida cewa ta je kasar waje ne ganin ‘yan’yanta da kuma likitanta, wanda ya kuma shawarce da ta dan ba da kanta hutu.

Tun da dare ne dai ‘yan jarida su ka yi dafifi a filin jirgin saman, inda su ke fatan yin tozali da kuma magana da Hajiya A’isha Buhari, nan da na bayan da su ka ji cewa ta na tafe.

Wannan zakuwa da ganin Aisha Buhari da ‘yan jarida su ka nuna, ya biyo bayan jita-jitar da aka yi ta yadawa, kama daga cewa A’ishar ta yi yaji ne zuwa kasar waje, zuwa cewa wai auren ta ne ya mutu, da kuma wai ana shirin mata kishiya, rade-radin da tuni majiyoyin fadar Shugaban Najeriya su ka yi watsi da su.

Ita ma da aka tambayeta kan wadannan batutuwan ta shiriritar da zancen.

To saidai, kamar yadda aka saba, wasu ‘yan jaridu na kwakwa, na cigaba da cewa idan ba rami, me ya kawo batun rami. Wasu kuma sun gamsu.

Karin hotuna daga dawowar A'isha Buharin.

VOAhausa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment